Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL ya kara rage farashin litar Man Fetur a kowace lita.
Ana sayar da man dai a baya kan N1,020, yanzu haka sun maida shi N 899
A cewar Ƙungiyar Ma’aikatan Tashoshin Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN), NNPCL ne ya sanya wannan sabon farashin.
Da ya ke nakalto wata takarda da Sashen Kasuwanci na NNPCL ya fitar, jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na ƙungiyar, Dakta Joseph Obele, ya bayyana cewa rage farashin ya danganta ne da tsarin farashi na yankuna, inda ya bayyana cewa, karkashin wannan tsarin, za a sayar da shi kan N970 a kowace lita a wasu sassan yankin Kudu maso Kudu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj