Wasu Kamfanoni Masu Gudanar Da Yawon Buɗe Ido, Sun Koka A Ofishin Jakadancin Najeriya Da Ke Ƙasar Saudiyya

Alfijr ta rawaito wadandu kamfanonin da ke gudanar da sufurin ayyukan yawon bude ido da suka shiga aikin Hajjin shekarar 2022 da aka kammala, sun kai kara zuwa karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Saudiyya kan rashin biyan bizar tafiya, tikitin jirgi da otal. masaukin da aka biwa wa wani kamfanin tafiye tafiyen na Saudiyya mai suna Alkahasafi Travel Tours Limited da Alshamel International Limited Company.

Alfijr Labarai

Alhaji Ibrahim Khaleel shugaban kamfanin Khaleel Travel Tours Limited ne ya bayyanawa jaridar Alfijr Labarai a yammacin ranar Litinin, a madadin sauran kamfanunuwan Abokanan Sana arsa da lamarin ya rutsa da su.

Khaleel ya nuna cewa kamfanonin tafiye tafiyen da abin ya shafa sun bukaci kamfanonin kasar Saudiyya da su maido da kudaden da suka kai sama da Naira miliyan 535 da aka biya a asusunsu domin yin hidima a lokacin. aikin Hajjin 2022.

Sun ce kamfanonin sun kasa yin ayyukan da aka amince da su yi yayin aikin Hajjin, don haka, ya zama wajibi a dawowa da masu hakki, kudadensu.

Alfijr Labarai

Ya kara da cewar, sun dauki dukkan matakan da suka dace don kwato kudaden daga hannun kamfanonin amma ba tare da wani sakamako ba, don haka an yanke shawarar shigar da karamin ofishin jakadanci da ya shiga tsakani don baiwa masu gudanar da yawon bude ido na Najeriya damar dawo da kwastomominsu hakkinsu.

. “Mun makala dukkan takardun ajiya a cikin wannan koke don tabbatar da ikirarinmu, wannan koken wata alama ce ta girmamawa da la’akari da muke da ita ga ofishin jakadancin Najeriya a matsayinmu na ‘yan Najeriya masu bin doka da oda,

Don haka muna kuma fatan kyakkyawan karamin daga ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya zai dauki batun kuma a magance shi cikin ruwan sanyi,” in ji Ibrahim

Alfijr Labarai

Ya ƙara da cewa, kamfanonin yawon shakatawa na Najeriya da abin ya shafa sun hada da Royal First Class Travel and Tours Services, Al Ansar Travels and Tours da kuma Khaleel Travel and Tours dake kano No 1. Civic Center

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *