Katu Ta Aike Da Wata Mata Mai Kai ’Ya’yanta Wajen ’Yan Bindiga Suna Lalata Da Su Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito An gurfanar da matar nan da ake zargi da kai ’ya’yanta mata wurin masu garkuwa da mutane suna lalata da su a gaban Kotun Majistare da ke Fada a birnin Zariya jihar Kaduna.

Alfijr

An gurfanar da Maryam Abubakar ne tare da Hajara Abubakar, ana tuhumarta da kitsawa da tsara yin garkuwa da mutane da safarar ’ya’yanta zuwa dajin Galadimawa, inda take kai wa Isa Dan Wasa don yin lalata da su, wanda hakan ya saba wa Sashi na 248 na kundin Manyan Laifuffuka na 2007. 

Wadanda ake tuhumar an ce sun hada baki ne suka yaudari wata Hadiza Musa suka kai ta wajen wani Rashidu Danfari shugaban dabar masu garkuwa da mutane ya yi lalata da ita wanda hakan ya saba wa sashe na 59 da 241 da 269 na dokokin Final Kod na Jihar Kaduna.

Alfijr

Bayan gurfanar da su gaban mai shari’a Zainab Garba Ahmad ta, dage sauraron karar sai ranar 10 ga Maris, 2022.

A ranar 21 ga Disamban bara ce ’yan sanda na musamman masu yaki da ’yan fashin daji da ’yan ta’adda (IRT), suka samu nasarar kama wadanda ake zargin su da safarar ’yan mata suna kai su wajen ’yan bindiga da ke dajin Galadimawa suna lalata da su.

Kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Slide Up
x