Wata Kotu A Kano Ta Ci Tarar Masu Tumatir A Kasuwar Sabon Gari Naira N50,000

Alfijr

Alfijr ta rawaito wata Kotu ta ci ’yan kasuwar tumatir da ke Kasuwar Sabon Gari a Jihar Kano tarar Naira dubu hamsin 59 sakamakon shakulatin bangaro da dokar tsaftar muhalli ta Jihar.

Alfijr

A safiyar yau asabar ce kotun tafi-da-gidanka da ke kula da tsaftar muhalli ta Jihar Kano ta sanya wa ’yan kasuwar tarar bayan ta same su suna gudanar da harkokinsu, lokacin gudanar da tsaftar muhalli ta karshen wata.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Auwal Suleiman Yusuf, shi ne ya yanke hukuncin bayan samunsu suna tsaka da harkokinsu, a lokacin zagayen tsaftar muhallin na yau.

Alfijr

Da yake yanke hukuncin, alkalin ya umarci shugabannin kasuwar ’yan tumatir din da su gabatar da kansu a hukumar muhalli ta Jihar Kano domin amsa tambayoyi.

Kotun, ta kuma ci tarar wasu kananan ’yan kasuwa da ta kama da laifin gudanar da kasuwanci a lokacin da dokar tsaftar muhallin ta karshen wata ta haramta.

Alfijr

Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dokta Kabir Ibrahim Getso a basa bayanin ya ce, gwamnatin jihar ba za ta lamunci karya dokar ba, ko duk wani abu da zai cutar da al’ummar Jihar Kano kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Slide Up
x