Masarautar Kano Ta Baiwa kamfanin Jirgin Air Peace kwanaki 3 Don Baiwa Sarkin Kano Hakuri

Alfijr

Alfijr ta rawaito, Isah Bayero shugaban tsare-tsare na masarautar Kano, ya baiwa kamfanin Air Peace sa’o’i 72 su baiwa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, hakuri bisa wulakantashi da suka yi da jinkirta tafiyarsa.

Alfijr

Malam Isah Bayero ya bayyana hakan ranar Asabar yayin hira da wasu manema labarai a jihar Kano, rahoton.

Yace wajibi ne kamfanin Air Peace ya amsa cewa yayi laifi wajen kin bin tsari, wanda haka ya janyo jinkirin Sarkin Kano a tashar jirgin garin Lagos.

Alfijr


“Tunda mun yi jinkirin zuwa daga Banjul awa guda, ya
kamata su sani da akwai
fasinjoji goma dake niyyar
zuwa Kano, kuma suyi abinda
ya kamata saboda ba laifinmu
bane jinkirin da ya faru.”


“Na kirasu sau da dama
amma suka ki daukan waya
sai daga baya sukace ba zai
yiwu ba.

Ya kamata shugabannin kamfanin su rikayiwa manyan mutane shiri namusamman.”


“Tun da sun jinkirta tashinmu
daga Banjul, wanda ya
Kawo jinkirin zuwa Lagos akan lokaci.


Ya kamata Air Peace ya shirya
yadda za’a damu. Amma babu
abinda sukayi.”

Muna masu basu sa’o’i 72 su baiwa mai martaba Sarki hakuri, na farko a jarida, na biyu kuma su turo
wakilai wajen Sarki.

Babu abinda ba zamu iya yi don
kare mutunci masarautarmu
ba.

A wasikar da Isah Bayero ya rubutawa kamfanin kenan.

Slide Up
x