Ya kamata Yan PDP Su Tsarkake Bakunansu Daga Kalaman Rashin Tarbiyya- Mal Shekarau

Daga
Bilkisu Yusuf Ali

Alfijr ta rawaito Jam’iyyar PDP wadda take babbar jam’iyyar hamayya da ke jihar Kano ta dau harama da saitin cin zabe a dukkan matakan takarkarin da ake da su a jiha da tarayya.

Taron da aka yi ranar 29/10/2022 taro ne da ya tattara dukkan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da ke jihar Kano kuma taro ne da babbar manufar sa ita ce, hadin kan ‘yan jam’iyyar inda za su zauna karkashin inuwar lema don samar da mulki da kawo sauyi na alheri, ba irin wanda ya haifar ma ta da da maras ido ba.

Taron ya hada da jiga-jigan jam’iyyar na PDP na jihar Kano kama daga kan jagoran jam’iyyar Malam tsohon Gwamna tsohon minista Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Bello Hayatu Gwarzo da Shugaban Shura Alh Dr Umar Maimansaleta da Ahaji Yakubu Yarima da Hajiya Baraka S Sani da Barista Adado da Malam Khalid Iman (chairman Atiku Writers Alliance) Dr Yunusa Adamu Dangwani da dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ta PDP Alhaji Sadik Imamu Wali da takwaransa Barista Alhaji Muhammad Abacha, da sauran dukkanin ‘yan takarkarin sanatoci da majalisar tarayya da ta jiha.

Yayin jawabin mai girma Sardaunan na Kano malam Ibrahim Shekarau, ya ja hankalin dukkan ‘yan jam’iyya da su zabi jam’iyyar PDP daga sama har kasa sannan su tsarkake bakunansu da zukatansu da dukkan wani abu na rashin tarbiyya ko sa’insa ko gaba da fadace-fadace.

Shekarau ya bayyana cewar burinmu a yi siyasa bada gaba ba.

Ya kuma nuna cewa da ma PDP ce gida ce kuma ya je ya dawo gida kuma zai yi iyakar iyawarsa don samun nasarar PDP.

A lokacin taron aka gabatar da shugabannin riko na jam’iyyar PDP na jihar Kano wanda caretaker chairman Mai Adamu Mustapha daga jihar Yobe da mataimakinsa Barista Habibu Adamu daga Kano sai sakatare barista Baba Lawan daga jihar Kaduna vice chairman Kano central Prof Mutari Banana sannan vice chairman Kano South Alhaji Abubakar Gwarmai, sai vice chairman North Auwalu Ibrahim Danzabuwa , sannan mukamin Odita Yakubu Lawan Yarima , PRO Alhaji Aminu Ibrahim D/Iya , Financial Sec Alhaji Aminu A Jingau , Ma’aji Alhaji Abdullahi Isa Ungoggo , Youth Kabiru Bello Dandago , Women Leader Hajiya Ladidi Dangalan da Organising Sec Alhaji Auwalu Isma’il Mai biskit. Inda wannan shugabanci ya fara aiki nan take.

A jawabin da Sanata Baraka sani ta gabatar ta nuna yadda jam’iyyar PDP uwa daya suke uba daya sannan ita ce tundun mun tsira a wannan zamanin.

Ta kuma yi kira ga jagororin jam’iyya da masu takara kan su tuna da mata su sa mata a kowannce tsari don sune kashin bayan kowacce nasara ta zabe kuma sune masu rauni.

Taron ya kayatar kwarai da gaske inda mutane daban-daban suka yi jawabi kan makomar PDP a jihar da tarayya da yadda jam’iyyar take kamshin dan goma sakamakon gazawa da cutarwa da jam’iyya mai mulki ta yi wa al’umma mai taken jiki magayi.

An kammala taro lafiya inda aka watse cikin farin ciki da girmama juna.

A nata bangaren Barista Adado muhimmancin hadin kan ta nuna da neman a tausaya wa mata a tafi kafada da kafada da su a duk inda za a je.

Daga Bilkisu Yusuf Ali
PDP Kano Stackholder
Chairperson National Women Alliance for PDP 2023

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *