Sulhu Ya Samu Tsakanin Alhassan Ado Doguwa Da Murtala Sule Garo

Alfijr ta rawaito Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a wani zama da suka yi na musamman a birnin tarayya Abuja, ya daidaita tsakanin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa da dan takarar mataimakin Gwamnan jihar Murtala Sule Garo bayan rikicin da ya bulla kai a tsakaninsu.

Idan zaku tuna a kwanakin baya ne dai aka zargi Alhassan Ado da harar Murtala Sule Garo da wani kofin shan Shayi, a lokacin da su Murtala Garo, suna tsaka da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a gidan mataimakin Gwamnan jihar kuma dan takarar gwamnan Nasiru Gawuna.

Wata sanarwa dai shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya fitar ga manema labarai, ya ce Gwamna Ganduje ya sulhunta tsakaninsu, inda ya ba da tabbacin cewa APC za ta cigaba da dinke duk wata baraka da ta kunno kai domin nasara a zaɓen 2023.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida, Ado Doguwa ya ce komai ya wuce, da fatan Allah ya kiyaye gaba kawai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *