Kotun Majistiri da ke zamanta a gini mai lamba 47 unguwar Norman’s land da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano ta aike da wasu ƴan TikTok biyu gidan yari na shekara guda amma da zaɓin tara.
Alfijir labarai ta rawaito cewa kotun ta samu ƴan TikTok ɗin biyu da laifin wallafa wasu bidiyo na rashin ɗa’a waɗanda suka ci karo da addini da kuma tarbiyyar jihar ta Kano.
Tun farko hukumar tace fina-finai ta jihar ce ta kame ƴan TikTok ɗin biyu waɗanda aka bayyana sunansu da Ahmad Isa da kuma Maryam Musa da suka fito daga unguwar Ladanai a yankin Hotoro na jihar, gabanin gurfanar da su gaban kotu.
Lauyan gwamnatin jihar Barista Garzali Maigari Bichi ya tuhume mutanen biyu da haɗa baki wajen aikata manyan laifuka baya ga wallafa saƙon da ya ci karo da tarbiyyar addini da kuma dokokin jihar ta Kano, laifukan da dukkaninsu suka amsa aikatawa.
Mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan da ta jagoranci zaman shari’ar ta aike da mutanen biyu gidan yari na shekara guda-guda amma da zaɓin tarar Naira dubu 100 kowannensu.
Hakazalika zaman shari’ar ya hori matasan biyu da su kasancewa masu ɗa’a da kuma bin dokokin jihar da addinin Islama.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ