Kotu Ta Bayar Da Sammacin Kama Ɗan Birtaniya Kan Yunƙurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu

Kotu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da sammacin kama ɗan ƙasar Birtaniya, Andrew Wynne tare da wasu ‘yan Najeriya bisa zargin cin amanar ƙasa da ta’addanci a lokacin zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa.

Alfijir Labarai ta ruwaito cewa mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da sammacin bayan ƙarar da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya shigar gaban kotun.

Sufeton ‘yansandan ya zargi zargi Wynne da wasu ƴan zanga-zangar 10 da aka tsare da laifin haɗin baki do nufin hamɓarar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da cin amanar ƙasa da tayar da zaune tsaye, da kuma ta’addanci, wanda ya saɓa wa sassa da dama na dokar ƙasa.

Waɗanda ake tuhuman, ana kuma zarginsu da hannu wajen shirya kai hare-hare da suka haɗa da ƙona harabar babbar kotu da ofishin NCC, da kuma gidan buga takardu a Kano.

A farkon wannan makon ne dai rundunar ‘yansandan Najeriya ta ayyana neman mista Wynne ruwa a jallo, bisa waɗannan zarge.

To sai a cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels Mista Wynne, ya musanta zarge-zargen tare da cewa zai amsa gayyatar ‘yansanda ta manhajar Zoom ko whatsapp.

BBC

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *