Wata kotun majistiri dake zamanta, a Kano ta bayar da umarnin tsare matasan da ake zargi da yin garkuwa da wani karamin yaro, mai shekaru hudu a duniya, har suka Nemi kudin fansar naira Miliyan 10.
Alfijir Labarai ta rawaito an karantowa matasan kunshin tuhumar da ake musu ta hadin baki da aikata laifi da kuma yin garkuwa da mutane, sai dai sun musanta zargin.
Wadanda ake zargin sun hada da Hisbullah Salisu mai Shekaru 30 da Hassan Ali Rabi’u mai Shekaru 28 dukkaninsu mazaunan unguwar Yakasai ne cikinkaramarhukumarbirni, sai kuma Hassan Ali mai Shekaru 22 mazaunin unguwar Hotoro Kano.
Tunda fari yan sanda ne suka kama su , sannan suka gurfanar da su a gaban kotun, bisa zargin yin garkuwa da karamin yaro mai suna Muhammed Nasir Jamilu, mazaunin Sharada Kano, a ranar 7 ga watan Satumba 2024, In da suka Kai shi karamar hukumar Gwarzo Kano, har suka karbi kudin fansar naira miliyan 10, amsa sun karbi naira Dubu dari Uku, Kafin a cika mu su ragowar kudin.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Rakiya Lami Sani, ta aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 30 ga watan Oktabo 2024 dimin ci gaba da shari’ar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj