Kotu Ta Tsare Wani Dan Kasuwar Kano, Sakamakon Badakalar $ 4,661 Ta Aiki Na Majalisar Dinkin Duniya

Alfijr ta rawaito Kotu ta ci gaba da tsare wani dan kasuwa a Kano kan damfarar Dala 4,661.

Alfijr Labarai

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa Ta’annati ta gurfanar da wani Ahmad Sultan Sardauna a gaban Mai Shari’a Farouq Lawal na Kotun Jihar Kano bisa tuhumarsa da aikata laifi guda daya.

Wanda ake karar da ya bayyana a matsayin dan’uwa ga Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya samu dala $4,661.60 (Dala Dubu Hudu da Dari Shida da Sittin da Daya, Centi Sittin) daga hannun wani Mista Ismail Jama, dan Somaliya, bisa zargin samun aiki, gare shi a Majalisar Dinkin Duniya.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *