Wata Kotu Ta Daure Wasu Matasa 5 Sakamakon Samun Su Da Laifin Karkatar Da Katin ATM A Kano

Alfijr ta rawaito Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Salim Mohammed Sarki da Sani M. Auwalu da Bashir Bashir Nasidi da Aliyu Mika’il Muhammed da Yahaya Abdullahi Abubakar (Shoki) hukuncin daurin mako biyu a gidan yari,dommin hada baki wajen sace kudi N1, 398,972.19.

Alfijr Labarai

Hukumar EFCC ta samu takardar koke, inda ake zargin an bude wani asusu da sunansa a wani banki na zamani ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.

Mai shigar da karar ya kuma yi zargin cewa ana amfani da wannan asusun ne wajen aikata zamba, ya kara da cewa, ƴan sanda sun kama shi ne a lokacin da ya isa bankin Jaiz don yin ciniki, daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Alfijr Labarai

Bayan karbar koken ne Hukumar ta fara bincike inda daga bisani ta gano cewa dan wanda ya shigar da karar, Sani Awwal ya sace katin ATM na mahaifinsa da katin SIM sannan kuma ya yi amfani da makamancin sa wajen sace Naira 100,000 a asusun bankin mahaifinsa.

Ya yi satar ne tare da taimakon sauran wadanda ake tuhuma.

Bayan gurfanar da su ne gaban mai shari’a, aka aike da su gidan gyaran hali da tarbiyya

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *