Kotu ta yankewa wani matashi hukuncin kisa saboda kashe budurwarsa

IMG 20260402 WA0778

Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zama a Uyo ta yanke wa wani mutum mai suna Ndifreke Isaiah Nelson mai shekara 33 hukuncin kisa bayan samunsa da laifin kashe budurwarsa.

Rahotanni sun ce Nelson, wanda jami’i ne mai kula da tsari a wata cocin zamani da ke Uyo, ya kashe budurwarsa mai suna Emem Monday Effanga a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, sannan ya gudu da wayarta.

An ce da misalin ƙarfe 7 na safe a ranar, Nelson ya je gidan marigayiyar da ke lamba 102, Aka Road da ke kusa da layin NEPA a Uyo domin amfani da wayarta wajen ɗora hotunan ranar haihuwarsa a kafafen sada zumunta.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke tsakaninsu kan wayar, inda ake zargin ya bugi kanta da bango sannan ya shake ta har ta mutu.

Bayan aikata laifin, Nelson ya tsere da wayar marigayiyar, amma jami’an tsaro sun gano shi a ranar 8 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 2 na dare a cocinsa da ke titin Nsikak Eduok Avenue a Uyo yayin wani taron ibada na dare.

A yayin bincike, an ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Ekpo Ntekim ya same shi da laifin kisa da sata tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allurar kashe rai. Kotun ta ce hukuncin satar ya shiga cikin hukuncin kisan da aka yanke masa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *