Kungiyar Mata Accountants (SWAN) Reshen Jihar Kano, Ta Karrama Haj Balaraba Ganduje

Alfijr

Alfijr ta rawaito Haj Asiya Balaraba Ganduje, na godewa Allah da irin yadda kungiyar SWAN ta zabo ta cikin dubban matan jihar kano, domin bata lambar karramawa.

Karramawar ta Haj Balaraba ta zo ne, yayin bikin kaddamar da shugabannin kungiyar mata akantan Najeriya (SWAN), reshen Kano.

Misis Christiana Oluranti-Danladi, ta zama shugabar kwamitin zartarwa da aka kaddamar a ranar Lahadin da ta gabata, ana sa ran kwamitin mai mambobi 11 zai jagoranci kungiyar na tsawon shekaru biyu masu zuwa.

Alfijr

Misis Danladi ta ce, bayan bincike da tayi, za ta inganta ilimin horarwa da ilimin kiwon lafiya ga mambobin, ta kuma yi alkawarin tabbatar da cewar ayyukan za ayi su har a cikin kana hukumomin jahar nan.

Ta ce shugabancinta zai ba da kulawa ta musamman wurin zaburar da matasa su shiga harkar aikin Akanta ta hanyar tarurruka da ba da horo.

Alfijr

A na sa bangaren tsohon shugaban Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria (ICAN) kuma shugaban bikin, Alhaji Isma’ila Zakari, ya taya sabbin zababbun shugabannin murna, inda ya bukace su da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Zakari wanda kuma mamba ne a hukumar Akanta ta kasa da kasa, ya ce cibiyar tana sa ran za su iya rike amana sosai, musamman ta fuskar aiyuka ga al’umma da kuma cibiyar.

Alfijr

Shugabar SWAN ta kasa, Misis Nwamara Nnaji, ta taya sabbin shugabannin kungiyar murna, inda ta bukace su da su bi ka’idojin adalci da gaskiya.

Ta kuma bukaci matan akanta da su jajirce wajen ganin an samar da zaman lafiya a kasar nan.

Alfijr

Kamar yadda Kano Focus ta halarci taron kuma ta wallafa a shafinta

Slide Up
x