Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano Yace! Sinadaran Hada Bam Ne Suka Haddasa Fashewa a Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan-sandan jihar kano ta ce fashewar da ta auku a wani shago a unguwar Sabon Gari da ke jihar a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, wadda ta hallaka mutum tara ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya hada bam da su ba silindar gas ba.

A tattaunawarsa da aka yi a wurin da ibtila in yabfaru a ranar, kwamishinan ‘yan-sanda na jihar ta Kano CP Sama’ila Dikko ya ce tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa.

kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar da wata sanarwa a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022, rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da wadannan haramtattun Sinadaran da ake hada bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar.

Alfijr

Sanarwar ta ce, binciken farko-farko ya nuna cewa daga cikin mutum tara da fashewar ta rutsa da su, daya daga cikinsu yana ajiye sinadarai masu lahani da sauran abubuwa masu hadari ba bisa ka’ida ba, wato Michael Adejo

Rundunar ‘yan-sandan tabbatar da mutuwar mutum tara da kuma wasu takwas wadanda suka hada da dalibai da suka samu raunuka a sanadiyyar fashewar ta ranar Talata.

Alfijr

Rundunar ta kuma bayyana wasu tarin durum-durum da jarkoki da ke dauke da sinadarai iri daban-daban, masu hadari da ta ce ta gano a inda lamarin ya faru.


Ta ce binciken kwararrunta a kan bam, ya nuna cewa suna zargin fashewar ta auku ne a sakamakon haduwar wasu sinadari da wuta.

Alfijr

Rundunar ta ce ta yi kame na wasu da ke da alaka da daya daga cikin shagunan da suka rushe a fashewar, wanda ake haramtaccen kasuwancin sayar da sinadarn da ababan da take zargi ana hada bam da su.

Ta kuma samu shedar sayen kayayyakin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Alfijr

Fashewar wadda ta auku a gida mai lamba 01 kan titin Aba/Court Road a unguwar Sabon Gari ya yi sanadiyyar rushewar gidan, wanda yake da shaguna hudu a kasa da kuma bene.

Akwai kuma wata makarantar boko ta yara, Winner Kids Academy a tsallaken gidan, inda da farko aka rika cewa a makarantar ne aka tayar da bam.