Kwankwaso Ya Ƙaddamar Da Manufofinsa Na Takarar Shugabancin Najeriya

Alfijr ta rawaito ɗan takarar shugaban kasa na jam`iyyar NNPP, Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya kaddamar da manufofinsa, wanda ya kunshi da hanyoyin da zai bi wajen aiwatar da su idan ya samu nasarar zama shugaban Najeriya.

Alfijr Labarai

Kwankwaso ya bayyana cewar zai rufe Hedkwatocin shugabannin tsaron ƙasar nan kaf, Tun daga Kan NPF, Land Army, AIR Force, Navy, NCS, NIS, DSS, NIA da suke à Abuja, domin shan AC, da aikin biro da takarda ya ƙare.

Ya kara da cewa, Zan mayar da hedkwatocinsu, wucin gadi a dukan jihohin da Tsaro ya fi ƙamari, Katsina, Zamfara, Kaduna, Sokoto, Maiduguri da Niger.

Za a raba su, kashi kashi, rukunin rukuni, su bi lungu da saƙo, kwazzabai, da ƙoramu, duwatsu da tsaunika, sarƙaƙiyya da duhuwa, itace da ciyawu, na duk wasu dazuka da ake zargin maboyar ƴan taddace, su fita neman su, ruwa jallo, su ka she kowa.

Alfijr Labarai

Madugun Kwankwasiyya ya ce, NIA da DSS su Nemi bayan sirri, ta amfani da security drones, divices antennas, motion didactors.

Su kuma Sojoji da haɗin guiwar Jami’an Tsaro, suna amfani da bayanan suna RUTHLESS OPERATIONS akan su.

Babu wanda zai dawo Abuja ofis, aikin biro da takarda har sai an ƙarar da duk wasu Ƙungiyoyi na ta’addanci a yankin Arewa da Nijeriya.

Alfijr Labarai

Hakazalika, Jami’an da ba sa iya yaƙi, saboda nauyin jiki, ko ƙiba, zan masu ritiya, domin buɗewa sabon jini hanyar samun aiki, idan kuma suna da ƙwarewa ta wani bangaren za a tafi da su.

Duk wasu sojoji da Jami’an tsaro da ke Barracks, da waɗanda aka tura wasu Ƙasashe aikin Kwantar da tarzoma, zan bayar da umarni a dawo da su gida.

Zan bayar da umarni, duk wasu ƴan ta’adda da aka kama, a jera su, a harɓe nan take, sannan à yi Video à sakawar kafofin yaɗa labarai, Domin ya zama izina ga na baya. In Ji Musa

Ya ƙara cewar, waɗanda kuma suka miƙa wuya, ko surrender, za ayi masu hukunci na abin da ya dace da su, ma fi sauƙi shi ne, Poison Injection.

Zan umarci, Hukumar National Emergency Management Agency (NEMA) da Federal Ministry of Humanitarian Services Disaster Management and Social Development. Su riƙa samar da camp-camps à dazukan da ake farautar yan ta’adda, tare da kai abinci da ruwa, ga Sojoji da Jami’an dake bakin daga à kullum.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *