Wani Kwanturolan Kwastam Ya Fadi Ya Mutu A Filin Jirgin Saman Kano

Alfijr ta rawaito Kwanturolan da ke kula da sashen kasuwanci na Hukumar Kwastam ta Ƙasa, NCS, Anthony Ayalogu, ya rasu.

Alfijr Labarai

A A Maiwada shugaban Sashin hulda da jama’a na hukumar kwastam, ya fitar, ya ce bayan da Ayalogu ya shiga mawuyacin hali, sai aka garzaya da shi asibitin sojojin saman Najeriya da ke Kano, inda a nan sai likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa.

Marigayin ya shirya tafiya ne kan wani aiki na hukuma kwatsam ta tura shi, daga saukarsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano sai kawai ya kamu da rashin lafiya, inda kafin kace kwabo ya suma.

“Duk kokarin da aka yi na farfado da shi bai yi nasara ba yayin da aka tabbatar da mutuwarsa a daidai ƙarfe 8:20 na dare a ranar Litinin, 17 ga Oktoba, 2022 a Asibitin Sojan Sama na Najeriya 465 Kano.

Alfijr Labarai

Marigayin ya rasu ne yana da shekaru 57, a duniya kamar yadda sanarwar ta wallafa.

A nasa bangaren Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali (rtd), yayin da yake jajantawa ‘yan uwa da abokan arziki Ayalogu, ya ce za a yi kewar marigayin sosai, saboda kyawawan halayensa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

2 Replies to “Wani Kwanturolan Kwastam Ya Fadi Ya Mutu A Filin Jirgin Saman Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *