Sama da mayaƙa 400 da suke addabar yankunan arewacin jamhuriyar Nijar ne suka miƙa wuya a birnin Agadez, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, ANP ta ruwaito.
Alfijir labarai ta rawaito rahoton ya ƙara da cewa mayaƙan ƴan ƙungiyar Patriotic Liberation Front da Movement for Justice and Rehabilitation of Niger ne.
An ce mayaƙan sun amince da kiran shugaban ƙasa Janar Abdourahmane Tchiani na miƙa wuya ne.
Ba a taɓa samun mayaƙa da suka kai wannan adadin ba, sannan a ranar 3 da 11 ga watan Nuwamba ma an samu irin hakan, inda wasu mayaƙan daban suka miƙa wuya a birnin na Agadez.
Mayaƙan suna faɗa ne tare da kira da a saki shugaban ƙasa Mohamed Bazoum da aka hamɓarar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj