Lugudan Wuta Da Rundunar Sojin Sama Ta Ƙaddamar Ya Hallaka ‘Yan Ta’adda 150 A Najeriya

IMG 20260106 WA0603

Daga Aminu Bala Madobi

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai mummunan hari ta sama a Jihar Niger, inda ta hallaka ‘yan ta’adda kimanin 150, bayan munanan hare-haren da suka yi wanda ya yi sanadin rasuwar fararen hula sama da 40 a ranar 4 ga Janairu, 2026.

Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin saman sun kai harin ne lokacin da ‘yan ta’addan ke kokarin tserewa daga sansanin su, bayan an gano motsin su ta hanyar bayanan sirri.

Jiragen yaƙin sojin saman sun kai farmaki cikin kwarewa, lamarin da ya jefa ‘yan ta’addan cikin mummunan kunci ba tare da samun mafita ba.

Rahotanni sunce wannan nasara ta rundunar sojan sama ta kara tabbatar wa da al’umma cewa gwamnati da hukumomin tsaro ba za su yi sassauci ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Jama’a na ci gaba da yabawa wannan gagarumar nasara, tare da fatan hakan zai zama darasi mai tsauri ga duk masu daukar makami suna barazana ga zaman lafiya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *