Daga Aminu Bala Madobi
Rahotannin dake iske sashin labarai na jaridar Alfijir ya bayyana cewa, Allah Ya kubutar matasan nan ‘yan Moriki da Bello Turji yayi holin su cikin bidiyo jiya tare da barazanar kashe su.
Cikin faifan bidiyon Turji yayi barazarar cewa zai kashe wadannan matasa a gobe Juma’ah in har mutanen Moriki ba su biya miliyan 30 da ya sanya musu dole biya ba.
Bayan zagawar faifan bidiyon, Turji ya canza sharawa inda ya ce abin ma bazai kai jumaa ba, domin yayi ikrarin zai kashe wadannan matasa da karfe 12:00 na ranar yau Alhamis idan ba a biya kudin ba.
Ko da jin haka wadannan matasa suka yanke shawarar guduwa cikin dare. Idan da sauran kwanakinsu su kubuta, idan kuma babu shikenan.
Rahotanni sun ce matasan sun sulale cikin daren jiya inda suka dinguma kungurmin daji suka gudu, Allah kuma ya kubutar da su.
Bayanai sun ce yanzu haka uku daga cikin wannan matasa tuni sun isa garin Moriki. Sauran biyun kuma, yanzu haka ana dakon isowarsu.
Sai dai har yanzu akwai mata guda shida ‘yan Moriki a hannun Turji, amma su dama su bai ce zai kashe su ba tukuna.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
Genuinely informating, educating and entertaining news body. Up mises browser!