Majalisar dattawa ta fara daukar matakai na maido da martabar kudin Najeriya ta hanyar haramta amfani da kudaden ƙasashen waje wajen biyan kudi da hada-hadar kasuwanci a cikin kasar.
Dokar da aka gabatar, da nufin tabbatar da duk biyan kuɗaɗe—da suka hada da albashi da sauran harkoki za a rika gudanar da su da Naira, wani yunkuri na neman farfaɗo da darajar kudaden cikin gida.
Wannan ya hada da sanya wajabcin biyan kudin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a Naira.
Sanata Ned Munir Nwoko, shugaban kwamitin majalisar dattijai kan farfaɗo da darajar duniyoyin kasa ne ya dauki nauyin daukar naa.
A cewar Sanata Nwoko, yawaitar amfani da kudaden waje a cikin tsarin hada-hadar kudi na Najeriya na lalata darajar Naira, tare da ci gaba da fuskantar kalubalen tattalin arziki.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj