Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙaddamar da sabon tsarin yaƙi da ta’addanci na ƙasa, shirin shekaru biyar da zai gudana daga 2025 zuwa 2030.Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da matsalolin tsaro ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar ciki har da satar mutane.
A cewar Akpabio, an tsara daftarin ne ƙarƙashin cibiyar yaki da Ta’addanci ta ƙasar, ƙarƙashin ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da nufin ƙarfafa tsaro da kuma tabbatar da cewa ƴan ƙasar na rayuwa ba tare da fargaba ba.
Ƙudurin ya ƙunshi cikakkiyar hanya ta sabunta tsarin tsaro na Najeriya, inganta hukumomin tsaro, da kuma gina ginshiƙan da zasu riƙe turakun tsaro a Najeriya, to amma shin zasu yi aiki? Tambayar kenan da na miƙawa masanin tsaro Yahuza Ahmed Getso masanin tsaro .
Sama da shekaru 10 kenan Najeriya ke fama da matsalolin tsaro, to amma a baya-bayan nan ana ganin tsanantar matsalar da ke da alaƙa da garkuwa da mutane.
RFI HAUSA
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t