Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince tare da damƙa ƙudirin ƙirƙiro Hukumar Inganta Tsarin Karatun Tsangaya, domin magance yawaitar yaran da ke gararamba ba su zuwa makaranta.
Alfijir Labarai ta rawaito Ƙudirin wanda a yanzu yake jiran Gwamnab Jihar ta Jigawa Umar Namadi ya rarraba masa hannu, za a kafa shi ya zama doka ne domin inganta tsarin karatun almajirci, wato karatun allo, ta yadda zai samu irin tagomashin tsarin karatun zamani a faɗin jihar Jigawa.
An amince da ƙudirin ya tsallake shingaye bayan Kwamitin Bai Ɗaya na Majalisa bisa jagorancin Kakakin Majalisa, Haruna Aliyu sun tattauna kan ƙudirin a ranar Alhamis.
Idan zaku tuna a watannin baya Gwamna Umar Namadi ya saka batun ƙirƙiro Hukumar Inganta Tsarin Karatun Tsangaya, a cikin Kasafin 2024.
Shugaban Kwamitin Inganta Ilmi a Matakin Farko, Ado Zandam, ya shaida wa manema labarai cewa tsarin karatun almajirai su ne aka ayyana waɗanda ba su zuwa makarantun zamani a jihar, duk da dai su na zuwa makarantun allo.
Ya ƙara da cewa hukumar wadda ake son kafawa za ta magance matsalar yara waɗanda ba su zuwa makaranta a jihar Jigawa, ta hanyar ƙarfafa masu guiwar haɗa karatun tsangayar da na zamani.
“Tsarin karatun Alkur’ani tsangaya daɗaɗɗen tsarin karatu ne a ƙasar nan tun kafin zuwan Turawa.
“Muna so mu inganta tsarin ta hanyar sama masa tagomashin haɗawa da na zamani, ta yadda za a zaburar da yara rungumar ilmi gadan-gadan. Hakan kuma zai kawar da su daga karakainar yawon barace-barace kan titina,” inji Zandam.
Cikin watan Yuli ne dai Gwamnatin Jigawa ta amince da haɗa gwuiwa da Gidauniyar Alfurqan ta Saudiyya, domin su inganta tsarin karatun tsangaya.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj