Majalisar Wakilai ta bankaɗo wata badakala a Kwalejin Kimiyya mai ɗalibai 142 da ma’aikata 154

IMG 20240213 WA0144

Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kwalejojin Kimiyya da sauran manyan makarantu ya gano cewa sabuwar Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Ugep, Jihar Cross River, na da dalibai 142 kacal tare da ma’aikata 154 na koyarwa da marasa koyarwa.

Alfijir labarai ta rawaito Kwalejin ta kashe kusan Naira miliyan 600 kan albashi da sauran kudaden gudanarwa, tare da kashe wani karin Naira miliyan 38 kan tafiye-tafiyen cikin gida.

Wannan gaskiya ta bayyana ne yayin da shugaban kwalejin, Farfesa Edward N. Okey, ya jagoranci shugabannin makarantar zuwa Majalisar a wani bincike na duba ayyukan da ke gudana.

A ci gaba da binciken da Kwamitin ke yi kan cibiyoyin ilimi karkashinsu, an gayyaci Kwalejojin Kimiyya na Tarayya da wasu cibiyoyin fasaha daga yankin Kudu maso Kudu, ciki har da Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Orogun; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ugep; Kwalejin Kimiyya ta Man Fetur da Gas, Bonny; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Auchi; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ekowe; Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Ukana; da kuma Cibiyar Gudanar da Fasahar Gina Gine, Uromi.

Shugaban Kwamitin, Fouad Laguda (APC, Legas), tare da sauran mambobin kwamitin, sun bayyana bacin ransu kan yadda Kwalejin da aka kafa a 2021 ke kashe makudan kudade don gudanarwa ga dalibai 142 kacal.

A bayanin da shugaban kwalejin ya gabatar a gaban Kwamitin, ya ce an yi amfani da Naira biliyan 2 da aka ba su a matsayin kudin fara aiki wajen gyara tsohon Ginin Makarantar Sakandare ta Al’ummar Ugep da aka yi watsi da ita don zama rikon kwarya, yayin da suke gina gine-ginen da suka karbe a Cibiyar Gudanar da Fasahar Kere-Kere (ITM) da yanzu ya zama sabon shalkwatar kwalejin.

Domin samun sauran shirye shiryenmu na Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *