Majalisar Dokokin  Jihar Kano Ta Nuna Kin  Amincewa Da Dokar Sake Fasalin Haraji

FB IMG 1733225580033

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi watsi da kudirin gyaran haraji da majalisar dokokin kasa ke nazari akai a halin yanzu.

An dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa a zauren majalisar, karkashin jagorancin  Jibril Ismail Falgore.

Shugaban masu rinjaye, Lawan Husseini, ya bayyana damuwarsa cewa kudirin zai yi illa ga tattalin arzikin yankin Arewa da kuma kara wahalhalun rayuwa.

Ya kara da cewa, shirin raba kudin haraji na VAT zai bada fifiko ga jihohi irinsu Legas, inda manyan kamfanoni ke da hedikwatarsu.

Lawal Husseini ya yi gargadin cewa hakan na iya raunana wasu jihohin Arewacin kasar, wanda  zai sa su wahalar biyan albashi da kuma kara fuskantar wahalhalun rayuwa.

Sauran ‘yan majalisar da suka hada da Honarabul Salisu Mohammed da Honarabul Murtala Kadage, sun goyi bayan kudirin, inda suka bukaci ‘yan majalisar Arewa da su hada kai game da wannan kudiri.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Sanatoci, da wakilai, da masu magana da yawun al’ummar jihar, da su nuna kin amincewa da kudirin dokar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *