Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta samu nasarar tabbatar da laifin Amir Zakariyya da Aliyu Hussaini kan tuhume-tuhumen hada baki, fashi da makami da kuma kisan kai a gaban babbar kotun jihar Kano.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta yanke hukuncin a ranar Talata a Kotu mai lamba 7 da ke Sakatariyar Audu Bako a Kano.
Kotun ta tabbatar da cewa da misalin karfe 2:47 na safiyar ranar 11 ga watan Yuni, 2025, wadanda aka yankewa hukuncin sun hada baki tare da kutsa kai cikin gidan marigayin, Yazid Haruna, a unguwar Sheka da ke Kano, inda suka kwace wayoyi guda biyu sannan suka kashe shi. Marigayin sabon ango ne, bai wuce kwanaki goma da yin aure ba a lokacin da lamarin ya faru.
Bangaren masu kara, karkashin jagorancin Lauyan Jiha, Lamido Abba Sorondinki, ya gabatar da shaidu uku tare da mikawa kotu bayanan furucin amsa laifi na wadanda ake tuhuma. Kotun ta yanke cewa an tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba.
An yanke wa wadanda aka samu da laifin hukuncin daurin shekara guda kan laifin hada baki, daurin rai da rai kan fashi da makami, sannan hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan kai. Kotun ta kuma lura cewa tuni suna zaman gidan yari bisa wasu laifuka makamantan haka bayan hukuncin da aka yanke musu a karshen shekarar 2025.
Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, ya jaddada kudirin ma’aikatar wajen tabbatar da an hukunta masu aikata laifuka yadda ya kamata. Ya ce sakamakon hukuncin na nuna aniyar gwamnatin Abba Kabir Yusuf na tabbatar da doka da oda tare da samar da adalci ga wadanda aka zalunta.
Sanarwar hakan ta fito ne ta hannun Abubakar Tijjani Ibrahim, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga babban lauyan jihar Kano.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t