Maryam Abacha American University Kano Na Sanar Da Masu Sha awar Shiga Jami ar Ga Dama Ta Samu

Ana sanar da dukkanin masu neman gurbin karatu a Jami’o’i daban-daban a Nijeriya a lokacin zangon karatu na 2021/2022 amma suke son su canza zuwa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, da su je ofisoshin JAMB a fadin kasar domin canza takardar shaidar shiga jami’o’i saboda har yanzu ba a kammala ba yana ci gaba da gudana.

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano tana mai kira ga wadanda suka zabi Jami’ar MAAUN a matsayin zabinsu na farko kuma suka sanya takardar shaidarsu a shafin JAMB da su je Fidelity Bank da ke fadin kasar nan su biya kudin fitar da shaidar gurbin shiga jami’ar (ADMISSION PROCESSING FEE) na Naira 32, 250 a lambar asusun Banki; Lamba; 5080133296 mallakar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya.

Ku bi shafin www.maaun.edu.ng domin aika bukatarku ta neman gurbin shiga jami’ar, sannan ku yi rajistar adireshin imel ɗinku da yake aiki kuma ku sanya duk takardun da suka dace, bayan haka, ku aika da bukatar nemanku ta hanyar yanar gizon domin la’akari da shi wajen ba ku shaidar takardar gurbin shiga jami’ar a hukumance wanda zai iya isa gare ku ta adireshin Imel dinku da kuka yi rajista da shi a yayin nema.

Alfijr

Ana mai sanar da cewa shafin Intanet na MAAUN yana aiki nan take inda dole ne ku biya kuɗin fitar muku da takardar gurbin shiga jami’ar kafin ku isa wurin inda takardar gurbin shiga jami’ar (admission) take.

Da fatan za a tabbatar da kun kammala rajistar ku ta hanyar sanya dukkanin takardun da suka dace da ake da buƙata ta hanyar shafin yanar gizon domin ba ku damar samun takardar shiga jami’ar, saboda kiris ya rage a fara tantancewa a ranar 14 ga watan Maris 2022, inda duk ɗaliban da suka samu takardar gurbin shiga jami’ar wadanda suka biya kuɗin karatunsu ko kuma waɗanda suka nemi shiga amma suke da matsala dukkansu za su bayyana tare da duk takardun da suka dace kuma ku kasance a shirye don biyan kuɗin da ake sa rai, duk za su kasance a yayin aikin tantancewa da adana takardun.

Alfijr

Hakazalika, hukumar gudanarwar Jami’ar tana son sanar da wadanda suka nemi Jami’ar cewa har yanzu za su iya zabar MAAUN tare da sanya takardun shaidarsu a JAMB portal domin samun gurbin shiga jami’ar.

SA HANNU:

Hukumar Gudanarwar MAAUN.

Slide Up
x