Gwamnatin Kano Ta Kori Wasu Ma’aikata Daga Bakin Aiki

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnatin jihar Kano ta sanar da korar wasu ma’aikatan hukumar ƙasa da safiyo ta jihar bisa samun su da laifin yin takardun bogi tare da sayar da wasu filaye mallakin hukuma.

Alfijr

Comishinan watsa labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya sanar da sallamar ma’aikatan a ranar Alhamis

Sanarwar ta ce kwamitin bincike da aka kafawa ma’aikatan ya gano cewa ma’aikatan sun yi amfani da takardun bogi da kuma sayar da filayen gwamnati wanda hakan ya saɓa da dokar aikin gwamnatin jihar Kano mai 04406.

Alfijr

Ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da

Abdulmuminu Usman Magami, mai matakin albashi na 6

Abdullahi Nuhu Idris mai matakin albashi na 10

Audu Abba Aliyu mai matakin albashi na 05.

Baba Audu mai matakin albashi na 13.

Alfijr

A ƙarshe sanarwar ta ja hankalin ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da su kasance masu bin doka da oda tare da gaskiya da amana.

Kamar yadda jaridar Kakaki Hausa Ta rawaito

Slide Up
x