Matasa sun wawushe abincin Ramadan da ɗan shugaba Tinubu zai raba a jihar Gombe

FB IMG 1742873878506

Wasu fusatattun matasa sun dakawa abincin da ɗan gidan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya je zai raba a jihar Gombe, kamar yadda ya ke a sauran jihohin Arewa da ya ke ta ziyar ta.

Alfijir labarai ta rawaito cewa a wani faifen bidiyo, an ga matasan sun yiwa motar dakon abincin dirar mikiya, inda su ka riƙa diba suna yin nasu waje.

An hango matasan da suke kan motar na jefawa wadanda su ke kasa kunshin abincin da ya kun shi shinkafa, sukari, man girki da taliya.

Daily Trust ta wallafa cewa mota biyu aka baiwa Gombe kason ta na kayan abincin da su ka kunshi katan 3,500 na abincin, inda bayan an raba mota daya ba gare da hatsaniya ba, dayar kima sai matasan su ka daka mata wawa.

Har zuwa hada wannan rahotan ba ta samu jin ta bakin jam’iyyar APC ba a jihar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *