Alfijr ta rawaito Wasu fasinjoji 14 sun kone kurmus a hanyar Gaya zuwa Wudil a wani hatsarin mota kirar Toyota Hummer da mota kirar Hyundai jeep.
Hukumar kiyaye haddura reshen jihar Kano sun tabbatar wa Solacebase cewa motar bas mai lamba GML 102 mallakin Kano Line ta taho ne daga jihar Gombe a yayin da ta yi karo da wata motar kirar jeep, da misalin karfe 7:30 na daren Lahadi.
Kwamandan hukumar FRSC reshen Kano, Zubairu Mato ya bayyana cewar, ranar Talata jami’an kiyaye haddura sun isa wurin da hadarin ya afku a kauyen Rege da ke Antukuwani, kan hanyar Kano zuwa Gaya da karfe 7:45 na yamma.
“Fasinjoji 13 ne suka kone kurmus nan take tare da jikkata wasu 6 a hadarin,” inji Mato.
An sanar da SOLACEBASE rasuwar daya daga cikin fasinjojin, macen da ta rasu a safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na Aminu Kano, (AKTH) Intensive Care Unit.
Kwamandan FRSC ya alakanta hadarin da gudun wuce gona da iri da wasu masu motocin ke yi.
Ya kuma bukaci direbobin da su tabbatar da amfani da na’urar da za ta iya kayyade saurin gudu a kodayaushe tare da kaucewa wuce gona da iri
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux