Kotu Ta Umarci A Yi Musu Bulalai Da Kuma Share Kotu, Bayan Bata Sunan Gwamna Ganduje

Alfijr ta rawaito kotun Majistare da ke zamanta a Kano a ranar Litinin ta yanke wa wasu mutane biyu Mubarak da Nazifi hukuncin bulala 20, da kuma yi wa al’umma hidima na tsawon kwanaki 30 bisa laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Ganduje.

Wadanda ake tuhumar, an same su da laifuka biyu da suka shafi bata suna da kuma tada hankalin jama’a.

Babban Alkalin Kotun, Aminu Gabari, ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin bulala 20 na sanda da kuma yi wa al’umma hidima na tsawon kwanaki 30, ciki har da shara da wanke-wanke na harabar kotun da ke Noman’s Land.

Mai Sharia Gabari ya kuma umarci wadanda aka yankewa hukuncin da su biya tarar Naira 20,000 kowannensu, da yin bidiyo a shafukan sada zumunta da kuma neman gafarar Ganduje.

Tun da farko dai, mai gabatar da kara, Wada Ahmad-Wada, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a watan Oktoban 2022 a shafukansu na sada zumunta na Tiktok.

Ya ce wadanda ake tuhumar sun wallafa a asusunsu na Tiktok cewa Gwamna Abdullahi Ganduje, ba ya ganin fili sai ya sayar da shi kuma yana barci da yawa.

Wadanda ake tuhumar sun amsa laifin da ake tuhumar su da su.

A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da tanadin sashe na 392 da na 114 na kundin laifuffuka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *