Najeriya ta karɓi bakuncin ‘yan majalisar dokokin Amurka inda suka nemi ƙarfafa haɗin gwiwa kan yaki da ta’addanci

FB IMG 1765126324807

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya karɓi tawagar ‘yan majalisar dokokin Amurka a ofishinsa da ke Abuja.

Ziyartar ta kasance ci gaban tattaunawar tsaro ta manyan jami’ai da aka gudanar a birnin Washington a watan da ya gabata.

Tawagar, wadda manyan mambobin majalisar suka jagoranta, ta haɗa da wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani da Riley Moore.

Ribadu ya ce Najeriya a shirye take ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da Amurka a fannin yaƙi da ta’addanci, da kuma bunƙasa ƙawancen tsaro na dabarun Najeriya da Amurka.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *