Nasiru El-Rufai ya musanta hannu a ɓacewar Dadiyata, ya dora zargi kan Gwamnatin Ganduje

FB IMG 1771079038712

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta zargin cewa yana da hannu a ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, tare da dora alhakin lamarin kan gwamnatin Kano a zamanin Abdullahi Umar Ganduje.

Idan za a tuna, Dadiyata ya ɓace ne tun ranar 2 ga Agustan 2019, bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun ɗauke shi daga gidansa da ke unguwar Barnawa a Kaduna. Tun daga lokacin ba a sake jin duriyarsa ba, duk da kokarin iyalansa da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam na neman a gano inda yake.

Da yake magana a wata hira da ARISE TV, El-Rufai ya ce Dadiyata ba mai sukar gwamnatin Kaduna ba ne, sai dai yana sukar gwamnatin Kano ne, yana mai cewa shi ɗan tafiyar Kwankwasiyya ne daga Kano.

Ya kuma bayyana cewa bai san Dadiyata ba sai bayan faruwar sacewar.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa, bayan wasu bincike da aka gudanar, an samu bayanin cewa waɗanda ake zargin sun sace Dadiyata sun fito ne daga Kano. A cewarsa, idan akwai wanda ya kamata a tambaya dangane da ɓacewar tasa, to gwamnatin Kano ta wancan lokaci ce ta fi dacewa da amsa tambayoyin.

Haka kuma, El-Rufai ya yi zargin cewa shekaru uku bayan faruwar lamarin, wani ɗan sanda da aka tura daga Kano zuwa Jihar Ekiti ya yi ikirarin cewa an aiko su daga Kano domin su sace Dadiyata, kuma daga bisani ya nuna nadamar abin da ya faru.

Har zuwa yanzu, babu wata hukuma da ta fitar da cikakken bayani kan inda Dadiyata yake ko halin da yake ciki.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *