NNPC Ta Biya Diyyar Filayen Aikin Bututun Gas na AKK, Ajakuta Da Kaduna Zuwa Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito, kamfanin Man Fetur na Kasa wato NNPC Kamar yadda ta alkawarta a yau Alhamis 17 ga Watan Feburairu 2022, ya sauke nauyin biyan diyyar gonakai da aikin jawo bututun Gas saga Ajakuta zuwa Kaduna zuwa Kano wato AKK Gas Pipileline Project ya biyo ta kai.

Alfijr


Bikin raba cakin kudin da aka yi shi a harabar Bankin Zenith dake titin Murtala Muhammad way a cikin garin Kano, ya samu Halartar manyan jami’ai daga Kamfanin karkashin jagoranci Alh Muhammad Isa, haka kuma Maigirma Mataimakin Karamar Hukumar Dawakin kudu da Dagacin kauyen Magami su suka jagoranci mazauna kauyen.


Bayan raba cakin kudin ga mutanen da aikin ya shafa, Maigirma Mataimakin Babban Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa domin aiwatar da aikin wato AKK – PDIC Hon. Mahmud A. Muhammad Tofa ya yabawa al’ummar kauyen da aikin AKK ya shafa da hadin kan da su ke bayarwa wajen samun nasarar aikin, sannan kuma ya yi musu albishir akan Karin kudi na kashi 50 akan kudin da Kamfanin Man Fetur na Kasa ya biya kowanne mai gona Wanda Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince ayi kuma za’a biya nan take.

Alfijr


Hon. Tofa ya kuma yi kira ga matasan kauyen da su hada Kansu domin su ci ribar arzikin da ya zo musu, daga karshe kuma ya gaya musu cewa kofar Kwamiti a bude ta ke ga duk wanda ya ga an raba masa gona kuma ba’a bashi diyya ba.


Malam Sulaiman Idris daya daga cikin wadanda suka karbi cakin kudin sa ya godewa Allah da ya nuna masa wannan rana da ya karbi kudin sa, sannan kuma yace shi dai tunda cigaba ne ya shigo yankin su ba shi da wani abun cewa sai Allah ya tabbatar da wannan babban aikin, kuma Allah ya sa su Mora.

Slide Up
x