Ramadan: Gwamnan Jihar Kano ya baiwa wasu kungiyoyin Yan jaridu tallafin  shinkafa buhu 450

IMG 20250310 152155

Gwamnan Jihar Kano ya baiwa wasu daga cikin kungiyoyin Yan jaridu tallafin  shinkafa buhu 450

Alfijir labarai ta ruwaito wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Sanusi Bature D-Tofa ya Sanyawa hannu.

Bature yace kungiyoyin da suka amfana sun hada da kugiyar ƴan jaridu ta ƙasa reshen jihar (NUJ) da kugiyar Jami’an hulɗa da jama’a ta ƙasa reshen jihar Kano (NIPR) da kugiyar mata ƴan jaridu (NAWOJ) da kugiyar maruba labarin wasanni reshen jihar Kano (SWAN) sauran sun haɗa da kugiyar ma.’akatan radio da talavijin da wasan kwaikwayo da kirkira (RATTAWU) da kugiyar shugabannin kafafen ƴaɗa labarai da kuma ASSOMEG kungiyar yan jaridu ta yanar gizo.

Raban ya gudana a cibiyar ƴan jaridu dake Farm Center dake jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Comr Ibrahim Abdullahi Waiya da mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature D-Tofa da wakilan kafafen ƴaɗa labarai da Kuma kungiyoyin.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *