Hedkwatar Tsaron Najeriya (Defence Headquarters, DHQ) ta karyata rahotannin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta da wasu gidajen labarai na yanar gizo, da ke cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da Brigadier Janar Tukur Gusau, Daraktan Yaɗa Labarai na Hedkwatar Tsaro, ya fitar a ranar Juma’a, rundunar ta bayyana cewa labarin babu tushe, babu ƙaƙƙautawa, kuma an kirkire shi ne da nufin haifar da tsoro, rudani da rashin amincewa tsakanin jama’a da jami’an tsaro.
“Hedkwatar Tsaro ta lura da wani rahoton karya da wata kafar labarai ta wallafa, wanda ke cewa soke bukukuwan cika shekara 65 da samun ‘yancin Najeriya na da alaka da yunkurin juyin mulki. Wannan ikirari yaudara ce kuma ba gaskiya ba ne,” in ji Janar Gusau.
Ya bayyana cewa dalilin soke taron ne domin bai wa Shugaba Tinubu damar halartar wani muhimmin taron haɗin gwiwar ƙasashe (bilateral meeting) a ƙasashen waje, da kuma bai wa dakarun soji damar mai da hankali kan yaƙin da suke yi da ta’addanci, ‘yan tawaye da kuma ‘yan bindiga a sassa daban-daban na ƙasar.
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa binciken da ake yi kan wasu jami’ai 16 da aka kama kwanan nan, al’amari ne na cikin gida domin tabbatar da ladabi da kwarewa a cikin rundunar, ba wani abu da ya shafi siyasa ba.
“An kafa kwamiti na musamman da ke binciken lamarin, kuma sakamakon binciken zai kasance a fili da zarar an kammala shi,” in ji DHQ.
Hedkwatar Tsaron ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su yi watsi da jita-jitar karya, tare da ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya a kokarinsu na kare ƙasar.
“Rundunar Sojin Najeriya tana nan daram cikin biyayya ga tsarin mulki da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya,” in ji sanarwar.
DHQ ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya, majalisa da bangaren shari’a na ci gaba da aiki tare domin tabbatar da tsaro, ci gaba da zaman lafiya a ƙasar.
“Demokraɗiyya za ta dawwama a Najeriya,” in ji rundunar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t