Hukumar DSS Ta Ja Hankalin ’Yan Jaridun Kano Kan Sahihai Da Ingantattun labarai

Alfijr ta rawaito Daraktan Tsaro na farin kaya DSS, jihar Kano Command Hassan .I Muhammad ya bukaci ‘yan jarida a Kafafen Yada Labarai da su hada kai da Hukumar wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da lumana a Najeriya.

Alfijr Labarai

Ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba 10/08/2022 a Kano lokacin da ya karbi bakoncin da mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Kano Online a ofishinsa.

A cewar Daraktan , shafukan intanet da na sada zumunta sun zama hanya mafi sauki ta yada bayanai wadanda miyagun mutane ke amfani da su wajen yada labaran karya, da labaran kanzon kurege da sauran sakonni masu tayar da hankali da ke iya haifar da rarrabuwar kawuna da tayar da tarzoma a tsakanin jama’a.

Ya ce, kasancewar kwararrun ‘yan jarida a Sabbin Kafafen Yada Labarai, ko shakka babu zai kawar da wadannan kalubalen da aka ambata a sama da Gwamnatin Tarayya ke ta kai kawo wajen magance su.

Alfijr Labarai

Daraktan ya ce, an dade ana tsammanin haduwarku a karkashin inuwa daya kuma an dade ana jira irin gudummawar da zaku bayar wajen magance wadannan matsalolin.

Don haka ta wannan kungiya za ku taimaka ta hanyar samar wa jama’a sahihin bayanai wadanda za su dakile munanan labaran da wasu marasa kishin kasa ke turawa”.

Muhammad, ya umurce su da su kiyaye dukkan ka’idojin aikin jarida yayin da suke ba da rahoton abubuwan da suka faru tare da la’akari da zaman lafiya da kwanciyar hankali na al’umma.

“Aikin ku yana da matukar mahimmanci, idan aka yi la’akari da rawar da kuke takawa a cikin al’umma, ku yarda da ni, mutane sukan yarda da ku fiye da kowace sanarwa na hukuma”.

Alfijr Labarai

Muna rokonku da, ka da ku shiga cikin rahotannin da za su dagula wa jami’an tsaro gwiwa da rudani.

Tsaro yana da fadi, ku ma za ku iya taimakawa wajen kare al’umma ta hanyar bayar da rahoton nasarori da ci gaba da kokarin da jam’i an tsaron kasar ke yi na tabbatar da tsaron Najeriya,” in ji shi.

Bugu da kari, ya yaba wa ‘yan kungiyar kan yadda ba su bari a yi amfani da su kwanan nan wajen yada jita-jita na harin da ba a tabbatar da shi ba a jihar wanda zai haifar da fargabar jama’a.

Alfijr Labarai

Daraktan na Jiha ya baiwa kungiyar tabbacin bada hadin kai da tsaro a yayin gudanar da ayyukansu.

Tun da farko, shugaban riko kuma sakataren kungiyar, Yakubu Salisu, ya ce suna kan umurnin da su gabatar da kungiyar tare da neman goyon bayan hukumar.

Ya ce, kungiyar da ta kunshi gogaggun ‘yan jarida da suka kware a kafafen yada labarai, an kafa ta ne domin daidaitawa da tsaftace ayyukan ‘yan jarida da ke aiki ta yanar gizo a jihar.

Waɗanda suka yiwa shugaban riko kuma sakataren kungiyar rakiya sun hada da

Alfijr Labarai

Abbas Yusha u
Musa Best seller
Abubakar Dangambo
Ibrahim Hamisu
Rabiu Musa
Hadiza Ado Jinta

Slide Up
x