Alfijr Labarai
Alfijir ta rawaito rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori wani dan sanda mai suna Liyomo Okoi da aka gan shi yana dukan wani mutum da bulala a cikin wani faifan bidiyo da aka yi a watan Yuli a social media
Alfijr Labarai
A cikin faifan bidiyon, Okoi na rike da bindigarsa a hannu daya kuma ya rike bulalar a daya hannun in da ya afkawa mutumin yayin da yake cewa, “Ya yi min barazana.”
Kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ya ce, “Rundunar ta kori jaminin mai lamba 524503 PC Liyomo Okoi da ke aiki a hedikwatar Ekori, rundunar ‘yan sandan jihar Cross Rivers bisa gallazawar da aka dauka a wani faifan bidiyo a ranar 31 ga Yuli, 2022 inda yana yi wa wani mutum bulala.
Alfijr Labarai
korar tasa ta fara aiki daga yau 8 ga watan Agusta, 2022.
Kamar yadda mai magana da yawun yan sanda ya fitar a yau
To gani ga wani ya isa wane tsoron Allah dai.