Sama da mutun Miliyan 60 a Arewa Suka Nuna goyon Bayansu ga Shugaba Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027

FB IMG 1729698661292

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027.

Alfijir labarai ta ruwaito fadar shugaban tace Sama da Mutanen Arewa Miliyan 60 Sun nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu, da Wasu da Kungiyoyi ga tuntuba ta matasan Arewa ta wakilta, sun bayyana Goyon bayansu ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sun jaddada cewa “goyon bayansu ga shugaba Tinubu da Sanata Akpabio, suna mai cewa “shugabannin biyu daga Kudu sun goyi bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban ƙasa da Shugaban majalisar Dattawa, kuma hakan ya dace a gare mu. don rama wannan gudummawar da suka bamu.”

Al’ummar Arewa, Sun yabawa shugaba Tinubu kan nasarorin da ya samu ta fuskar bunkasa karfin dan Adam da ababen more rayuwa, irin su babban titin bakin teku, hukumar raya Kudu maso Gabas, Asusun NYSC Trust Fund, da kuma tsarin lamuni na dalibai a matsayin shaida na jagorancin gaba na Tinubu a karkashin shirin Renewed Hope. Yusuf ya yarda cewa, duk da kalubalen tattalin arziki, Gwamnatin Tinubu ta tafiyar da harkokin kasar yadda ya kamata ba tare da tara basussuka da ya wuce kima ba.

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa ta yi kira da a baiwa gwamnati hakuri da kuma hadin kai a yayin da ake ci gaba da kokarin gina Najeriya mai inganci.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *