Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi Kira ga al’uma su cigaba dayin addu’oin samun zaman lafiya bisa muhimmacin da yake dashi a cikin al’uma.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya jagoranci wani taron gamayyar kungiyoyi a fadarsa dake Gildan Sarkin Na Nasarrawa a Kano.
Yace da zaman lafiya ne al’uma suke samun dukkan wani cigaba da habakar arziki, amma idan babu zaman lafiya to baza’a samu cigaba ba Sai dai koma baya.
Ya yabawa shugabar lauyoyi Mata Barista Nafisa da shugabar Mata masu Da’awa bisa Jawaban da Suka gabatar a wankan taron, kazalika sarkin ya godewa Allah bisa yadda ya canza wannan taro da haye hayen sallah duk kuwa da irin muhimmacin da hawan sallah yake dashi a al’adar masarautar kano.
An dai gabatar da jawabai daban daban a wajan taron tareda mika gudunmawar sabuwar Mota ga masarautar Kano daga Babban Darakta Baffa Babba Dan Agundi.
Sa Hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.
1/04/2025
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD