Sauya sheƙar Gwamnan Kano zai ƙarfafa haɗin kan Arewa maso Yamma  – In Gwamna Radda

FB IMG 1769793769456

Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso yamma, Umaru Radda, ya bayyana sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC a matsayin mataki na dabaru da zai iya ƙarfafa zaman lafiyar siyasa, haɗin kai da ci gaban yankin baki ɗaya.

Radda ya ce sauya sheƙar Yusuf na nuna kishin ƙasa da jajircewa a wani lokaci da ake buƙatar ƙarin haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya domin tinkarar ƙalubalen tsaro, tattalin arziƙi da zamantakewa da ke addabar Arewa maso Yamma.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar Laraba, Radda ya ƙara da cewa sauya sheƙar za ta zurfafa haɗin kai da gwamnatin tarayya tare da ƙarfafa aiwatar da Ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin amfanin Jihar Kano.

Yayin da yake jaddada muhimmiyar rawar da Kano ke takawa a fagen siyasa da tattalin arziƙin Arewa maso Yamma, Radda ya nanata cewa shigar Yusuf APC zai ƙarfafa haɗin kan yankin, daidaita manufofi, da haɗin gwiwar aiki tsakanin jihohi.

Ya ce wannan sauyin matsayi zai ƙara inganta haɗin kai a muhimman fannoni kamar tsaro, sauya fasalin noma, masana’antu, da bunƙasa matasa, tare da inganta samun shirye-shiryen tarayya da zuba jari.

Daily Nigerian Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *