Shugaban Ƙasar Faransa ya zargi Amurka da Isra’ila da saɓawa dokokin duniya wajen afkawa Iran

FB IMG 1772576542758

Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya ce babu tantama Amurka da Isra’ila sun saɓawa dokokin duniya wajen kai hari ƙasar Iran, abinda ya haifar da yaƙin da ke gudana yanzu haka wanda ba su amince da shi ba.

Sai dai shugaban ya kuma zargi Iran da alhakin haifar da wannan matsalar dangane da abinda ya shafi shirin nukilyarta da goyan bayan ayyukan ta’addanci a yankin, tare da harbe jama’ar ƙasar ta dake zanga zanga a watan Janairu.

Shugaban Faransa ya sanar da cewar ƙasar sa ta tura katafaren jirgin ruwan dake ɗaukar jiragen yaƙi Gabas ta Tsakiya domin tabbatar da tsaro a yankin, sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran.

Yayin da ya ke jawabi ga al’ummar ƙasar, Macron ya ce sun yanke hukuncin ɗaukar matakin ne na tura ‘Charles de Gaulle’ mai ɗauke da jiragen yaƙi na Rafael Jet saboda abinda ke faruwa a yankin.

Macron ya ce sakamakon yarjejeniyar tsaron da suke da shi tsakanin Faransa da Kuwait da Bahran da kuma Daular larabawa, sun tura na’urorin kakkaɓo makamai domin kare su daga makaman da Iran ke harba musu.

Shugaban ya ce daga cikin makaman da za su tura yankiin harda wanda za’a kai Cyprus, kasar da ke ci gaba da fuskantar barazana daga Iran.

Macron ya tabbatar da cewar Faransa ta kakkaɓo wasu daga cikin makamai masu linzamin da Iran ta harba, ba tare da ƙarin bayani akai ba.

Shugaban ya kuma nuna rashin amincewarsa da shirin Isra’ila na tura sojoji ckin ƙasar Lebanon, abinda ya kira a matsayin babbar takala mai tattare da kura kurai.

Macron ya ce a cikin daren yau ake saran saukar jiragen sama guda biyu ɗauke da ƴan Faransa da aka kwaso su daga yankin da ake gwabza yaƙin.

RFI Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *