Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya taya Mojtaba Khamenei murna kan naɗinsa a matsayin sabon jagoran addinin Iran, tare da tabbatar da goyon bayansa ga ƙasar.
A cikin saƙon taya murna da aka wallafa a shafin Kremlin, Putin ya ce: “ina miƙa gaisuwa ta ta musamman tare da taya Mojtaba Khamenei murna kan naɗinsa a matsayin jagoran addini ta Iran.”
Shugaban Rasha ya ƙara da cewa yana tabbatar da goyon bayansa ga ƙasar Iran tare da taimaka mata ba tare da shakka ba” sannan ya yi alkawarin “ci gaba da zama abokin ƙasar mai aminci.”
“A wannan lokacin da Iran ke fuskantar hare-hare mai girma, tabbas za su bukaci ƙarfin zuciya da sadaukarwa. Ina da yaƙinin cewa za ka ci gaba daga inda mahiafinka ya tsaya cikin girmamawa, kuma ka haɗa kan al’ummar Iran a wannan mawuyacin lokaci,” in ji shi.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t