Siyasa! Wani Shugaban Karamar hukuma ya fita daga APC ya koma NNPP a Kano

IMG 20240206 122028

Shugaban Karamar hukumar Nasarawa Auwal Lawan Shu’aibu wanda aka fi sani da aranposu ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP mai mulkin jihar Kano.

Alfijir labarai ta rawaito Aramfosu na cewar Ungulu ta Koma gidanta na Tsamiy, Kuma fa His Excellency “ABBA KABIR” Masoyin talakawa ne da Kano, mu ci gaba da taya shi da adu’a” don cigaban jihar.

Auwal Lawan ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook a safiyar talatar nan.

Tun da sanyin safiyar wannan rane dai aka wayi gari da wasu hutunan shugaban karamar hukumar ta Nasarawa da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf yayin wata ziyara da ya kai masa.

A hotunan an ga Aranposu sanye da jar hula Wanda hakan Ke nuni da cewa ya koma tafiyar Kwankwasiyya da ya bari tun lokacin da aka raba gari tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Dama dai Aranposu yayi kaurin suna wajen sukar dan takarar gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC duk da sun fito a karamar hukuma guda.

Kwanaki kadan ne dai suka ragewa shugabannin kananan hukumomi a jihar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *