Alfijr ta rawaito dakarun sojin Najeriya da ke aiki da ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ɗaya daga cikin gawurtattun ƴan fashin daji da suka yi kaurin suna a Zamfara.
Alfijr Labarai
kwamandan ƴan bindigan da aka bayyana sunansa da Ibrahim Chire, ya addabi yankunan Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka, In ji shi.
Gen. Must Danmadami, wanda ke zaman daractan yaɗa labarai na hukumar a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis, ya bayyana cewa an kashe dan ta’addan ne a yayin wani artabu da sojoji suka yi.
Ya ce an kuma kashe wasu ƴan ta’adda biyu yayin da mabiyansu suka gudu da raunukan harbin bindiga.
Danmadami ya bayyana cewa, “Rundunar Operation HADARIN DAJI sun gudanar da sintiri na yaki da ‘yan bindiga a dajin Doka da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara a yau 20 ga watan Oktoba 2022.
Alfijr Labarai
Sojojin sun afka wa ƴan Ta’adda ne lokacin wani Sintiri da suka gudanar, kuma sun yi ta harbi. Dakarun da ke aikin sun kashe ‘yan ta’adda biyu yayin da wasu kuma suka gudu da raunuka.
Yayin da ake bincika yankin gaba daya, an gano daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe da sunan Ibrahim Chire, wani shahararren shugaban ‘yan bindiga da ya shahara wajen ta’addancin Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka.”
Daraktan ya kara da cewa daga baya sojojin sun kwato AK 47 daya, da harsashi mai girman 7.62mm, Babur daya, wayoyin hannu da dai sauransu.
Alfijr Labarai
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller