Alfijr ta rawaito Sojoji a ƙasar Burkina Faso sun hamɓare shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a ranar Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata.
Alfijr Labarai
Sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau.
Haka nan sun dakatar da aiki da kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma rusa gwamnati mai-ci.
Idan za ku iya tunawa tun a watan Janairu ne Kanar Damiba ya hau mulki bayan ya jagoranci juyin mulki da yayi.
Da Safiyar Juma’a aka ji ƙarar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Burkina Faso da kuma hedikwatar sojojin juyin mulki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya sanar.
Alfijr Labarai
Sanarwar ta ce, Ssojoji sun tare manyan hanyoyin da suke babban birnin ƙasar Ouagadougou.
An jibge dakarun tsaro a manyan hanyoyin da ke yankin da fadar shugaban ƙasar da hedikwatar sojojin suke.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller