Ta Dabo: Yan Majalisar Wakilai 7 daga jihar Kano sun sauya sheka daga NNPP zuwa APC

IMG 121758 201025 1760959086441

‘Yan Majalisar Wakilan na Jihar Kano sun sanar da sauyin shekar ne a wasu wasiku da Shugaban Majlisa Abbas Tajuddeen ya karanta a Zauren Majalisar ranar Talata

Wasu jiga-jigan jam iyyar ta APC daga Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf sun halarci zaman majalisar don shaida sauyin shekar.

Tun da farko sai da Shugaban Majalisar ya yi wa manyan baƙin iso gabanin shigowar su.

A wasiƙun da suka aike wa Shugaban Majalisa Tajuddeen Abbas, wakilan sun bayyana rikicin shugabanci da rashin makoma a matsayin dalilan da suka sanya su sauya sheƙa zuwa jamiyyar APC.

Wakilan sun hada da Honarabul Gali Mustafa Tijjani mai wakiltar kananan hukumomin Gaya da Albasu da Ajingi; da Honarabul Muhammad Bello Shehu mai wakiltar Karamar hukumar Fagge; da Honarabul Idris Dankawu mai wakiltar Karamar hukumar Kumbotso.

Sauran sun haɗa da wakilin Karamar Hukumar Nassarawa, Honarabul Hassan Shehu Husaini; da na ƙananan hukumomin Sumaila da Takai, Honarabul Rabi’u Yusuf; da na Gabasawa da Gezawa, Honarabul Muhammed Ciroma.

Sai kuma Honarabul Garba Ibrahim Muhammad, mai wakiltar Karamar Hukumar Gwale.

Wannan sauyin sheka dai yana zuwa ne kwana guda bayan jagoran jam;iyyar ta NNPP kuma dan takararta a zaben Shugaban Kasa na 2023, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheka zuwa jam;iyyar adawa ta ADC.

Blueprint Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *