Daga Bilkisu Yusuf Ali
Chairperson National Women Allience For PDP 2023.
Alfijr ta rawaito ranar 5 ga watan Nuwanba 2022 Malam Ibrahim Shekarau ya cika shekaru 67 cif da zagayowar ranar haihuwar ta dace da lokacin da Malam Shekarau yake kamshin turare dan goma a jam’iyyar PDP.
WA YE MALAM IBRAHIM SHEKARAU?
An haifi malam Ibrahim Shekarau a Unguwar Kurmawa a cikin birnin Kano, ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 1955.
Sunan mahaifinsa Malam Sulaiman Usman, mahaifiyarsa Hajiya Maryamu.
Mahaifinsa jami’in tsaro ne, ya yi aikin dan sanda na tsawon shekara 35 a tsarin ‘yan Doka da aka fara yi tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Kuruciyar Malam Ibrahim Shekarau ya yi ta ne a hannun Iyayensa, in da ya fara da karatunsa na allo kamar yadda aka saba a kasar Hausa, daga nan ya shiga makarantar firamare ta gidan Makama.
Ibrahim Shekarau Ya yi sakandire a Aminu Kano Commercial College, daga nan ya tafi jam’iyyar Ahmadu Bello da ke Zaria daga shekarar (1973-1977) Ya samu takardar shaidar digiri ta farko.
Bayan kammala digiri sai ya fara aikin gwamnati, a makarantar Government Technical College da ke Wudil a shekarar 1978, bayan shekaru biyu ya zama shugaban makarantar Government Day Junior Secondary School a Wudil A shekarar 1980.
Shekarau Ya koma makarantar Government Secondary School, Hadejia da Government College Birnin Kudu a 1986 da Government Secondary School a Gwammaja da Rumfa College a 1988, duk a matsayin shugaban makaranta.
A shekarar 1992 mallam Shekarau ya zama mataimakin darakta a harkar illimi.
Bayan shekara guda da mayar da shi darektan, ya zama babban sakatare a ma’ikatar harkar illimi.
A watan Fabrerun shekarar 2000, malam Shekarau ya koma aikin gwamnati, kafin a komar da shi kwalejin share fagen shiga jam’ia a matsayin babban malamin lissafi.
A nan dai Malam Shekarau ya ajiye aiki da gwamnati bayan ya yi aikin na tsawon watanni 17 a kwalejin.
MALAM IBRAHIM SHEKARAU DA SIYASA.
Akwai mutane da ake kira ‘yan baiwa a rayuwarsu, hakika malam Ibrahim Shekarau yana cikinsu musamman idan aka kalli irin tasirinsa a siyasa lokaci guda.
Da farko ba a dauki Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wani dan takara da zai yi tasiri ba a zaben gwamnan da aka yi a shekarar 2003 a jihar, amma daga baya kuma sai ya yi tasiri inda ya lashe zaven.
Malam shekarau ya kafa tarihi inda ya zama gwamna na farko da aka zabe shi a karo na biyu a matsayin gwamna a jihar Kano.
Malam Ibrahim Shekaru ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyar ANPP a Zaben watan Afrilu na shekarar 2011.
Malam Ibrahim Shekarau ya rike mukamin ministan Ilimi a zamanin shugabancin Goodluck a karkashin jam’iyyar PDP.
Shekarau ya zama Sanatan Kano ta tsakiya a shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar APC zuwa lokacin da ya bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar NNPP bisa wasu dalilai wadanda suka shafi rashin cika alkawari da mutumta zamantakewa ta siyasa daga jam’iyyar APC.
Hakazalika a jam’iyyar NNPP din ma hakan ta kuma faruwa, bayan zama da tuntubar magoya baya, suka yanke shawarar komawa gidansa na baya wato jam’iyyar PDP.
Bahaushe ya ce, Inda aka san darajar goro nan ake yyayafa masa ruwa.
Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar ya isa Jihar Kano tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da Shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, da sauran shugannnin jam’iyyar na kasa da duk masu fada a ji a jam’iyyar ta PDP suka shigo takanas don karbarsa a jam’iyyar ta PDP.
A yayin taron ne, aka jiyo tsohon gwamnan jihar Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana matakin da ya dauka na barin jam’iyyar NNPP da komawa jam’iyyar PDP ya yi shi ne a dalilin yaudararsu da dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso.
Shekarau ya yi ikirarin cewa jagoran jam’iyyar NNPP bai yi musu adalci ba. dangane da yarjejeniyar da suka kulla kafin komawarsa jam’iyyar.
SARAUTA
Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya zabe shi a matsayin Sardaunan Kano a karon farko a tarihin masauratar Kano.
Wanda ya ci gaba da bawa Masarautar Kano gudummawa da kulawa tun yana kujerar Gwamnan Kano har zuwa yanzu.
HALAYYAR MALAM SHEKARAU DA TA BAMBANTA SHI DA SAURA
Mal Shekarau ya na da hakurin da ba za ka tava jin malam Shekarau na fada da kowa ba , ko da kuwa an tsokane shi ko an ci fuskarsa yana kau da kai.
Don haka kullum akan ji harshen masu adawa da shi ne amma shi ba a jin martaninsa Kawaici da ko da abu zai cuce shi zai yi hakurin juriya, abin da ya sa kaji ya mai da martani to abu ya kai intaha.
Shekarau shugaba ne da ya yarda da cewa shugabanci sai da jin korafin magoya baya, sannan ba ya yanke kowanne hukunci sai ya ji shawararsu, domin ya ba su damarsu.
Haka nan kuma bai yarda da shugabanci na kama –karya ba.
Tun yana gwamna har zuwa yau.
Malam Ibrahim Shekarau bai yarda da cewa siyasa ta marasa kunya ce da surutai barkatai kamar a tasha ba.
Don haka ya sa dokar tsarkake harshe da duk abin da za a fada, sai an sa ladabi a ciki an kyautata magana tamkar a masallaci mutum yake, ko da kuwa yana kan dandamalin siyasa ne wato (kamfen)
Malam Ibrahim ya fara janyo malam addinin Musulunci da daliban ilimi cikin harkar siyasa don maye gurbinsu da marasa tarbiyyar da suke daukar siyasa ta su ce, da ‘yan boko akida da marasa ilimi.
Kuma hakan ya kara tsaftace siyasa har ya ja hankalin mutane masu daraja ga siyasa ganin irin su malam da mukarraban gwamnatinsa a siyasa.
Kowa ya shaidi malam Ibrahim Shekarau akan kansa ba barawo ba ne.
Saboda kuwa irin tsangwama da yarfe da yadda ya zame wa wasu tarnaki da yana da laifi komai kankantarsa da sun bi duk inda za su bi su kama shi ko su wulakanta shi.
Malam Shekarau shi ne mutum daya da magoya bayansa ke girmama shi don nutsuwarsa da kamalarsa da kyakkyawan lafazinsa ba wai don rudu ko don farfaganda ba.
Masoyan malam duk inda suke za ka iske su nutsattsu da soyayya don Allah ba don kudi ba ko mukami.
Wannan ya sa magoya bayansa ko da sun sami sabani na siyasa ba za ka taba jin sun aibata shi ba a fili ko a boye ba.
Shi yana rike su a matsayin amana kuma uba, haka suma sun yarda shi jagoransu ne, ko suna jam’iyya guda ko a’a.
Shugaba ne, na mutane don haka gidansa yake a bude ba a rufe shi yana gari ko ba ya gari.
Gidan hedikwata ce kuma fada ce sannan munbari ne na wa’azi da siyasar zamani.
Mai gaskiya ne da saurin sallamawa da yarda da mutane da zama da su zuciya daya, wannan yana cikin dalilan da ya sa ‘yan siyasar zamani ke sauran yaudararsa.
Lokuta da dama magoya baya da masoya kan masa kirari da cewar “Bangon sikari kirarinsa kenan.”
Don kuwa ba wanda zai rabi malam Shekarau bai amfana ba.
Babban abin farin cikin da irin kyautar nan da addini ya yi umarni wato ka bayar da kyauta da hannun dama , hagun bai sani ba.
Muna fatan Allah ya ja kwana, ya kara lafiya da daukaka al’ummar Kano, Al’ummar Arewa da ma al’ummar Nijeriya su ci gaba da amfanar wannan tsiro na albarka amin.
Mai girma Sanata Allah ya kai fata mizani.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux