Tashin Tashina: Jaruma Maryam Malika ta roƙi kotu da ta tabbatar da sakin da mijinta ya yi mata

FB IMG 1739475592570

Jarumar masana’antar fina-finai ta Kannywood, Maryam Muhammad, wacce aka fi sani da Maryam Malika, ta roƙi wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna da ta tabbatar da sakin auren da tsohon mijinta, Umar ya yi mata.

Jarumar, wacce lauyanta A.S Ibrahim ya wakilta ta shaida wa kotun, a jiya Laraba cewa wanda ake kara ya furta saki na uku tun shekaru biyar da su ka gabata bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i (hakkin mace na ta nemi saki a Musulunci).

“Ya yi furuci na saki biyu ne bayan wanda na ke karewa ta shigar da kara a kotu ta na neman saki ta hanyar Khul’i.

“Kotu ta aika masa da takardar umarni kuma a kai ya rubuta saki na uku, inda wacce na ke karewa ta kuma ci gaba da harkokin ta ba tare da ta dawo kotu ta tabbatar da hakan ba,” in ji shi.

Wanda ake tuhuma ba ya cikin kotu kuma bai aika da wani wakili ba.

Alkalin kotun, Kabir Muhammad, ya tambayi dan aiken kotun ko ya baiwa wanda ake kara takardar umarni sai ya amsa cewa wanda ake kara ba ya gida a lokacin da ya je kai masa takardun daga kotun.

Alkalin kotun ya umurci jami’an kotun da su sake aikewa wanda ake kara takardar umarni ta wasuhanyoyin sannan ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *