Alfijr ta rawaito Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.
Alfijr Labarai
Asiwaju ya bayyana haka ne a ziyarar kwanaki da ya kai jihar Kano, ya bayar da gudunmawar ne a lokacin liyafar cin abinci da kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano ta shirya masa domin karrama shi.
Ya ce sun bayar da tallafin ne domin taimakawa da rage radadin ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa.
Hakazalika ya yi alkawarin sake mayar da masana’antun da ake da su a matsayin tushen ci gaban masana’antu da bunkasu a Arewa da kasa baki daya.
Alfijr Labarai
Tinubu ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar.
Ya kuma yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller